LIFE HELPERS TA GABATAR DA TARO AKAN AIBIN SAYAR DA ƘURI'A

Ƙasa ga watanni uku da suka rage kafin babban zaben shekara ta 2023. Hadaddiyar kungiyar nan mai zaman kanta watau (Life Helpers Initiative) ta gudanar da taron wayar da kai ga shuwagabannin kungiyar mata ta 100 women group, a kan lahani da kuma illar sayar da katin zaɓe.

An gudanar da taron ne ofishin kungiyar dake jahar Sakkwato a unguwar Tamaje a ranar juma'ar da tagabata. 
Mahalarta taron sun tattauna a kan matsalolin dake haifar da sayar da katin zabe.
Tare da matsalolin dake addabar mata wadda ke tilasta su sayar da katin zabe.
Mai jagorantar zaman wayar kan, Hajiya Hadiza Yaro, ta gabatar da tambayoyi ga mahalarta taron a kan matsalolin da kuma hanyoyin da za iya bi wajen dakile wannan matsalar.
"Shin idan talauci ya sanya ku sayar da kuri'unku a zaɓen da ya gabata, shin kuɗin sun fitar da ku talaucin ko har yanzu jiran wani zabe kuke yi domin karɓar dari biyu ko Naira dubu?" A cewarta.
A nata tsokacin a kan wannan batun, shugabar Kungiyar mata ta 100 women group reshen ƙaramar hukumar mulkin Shagari. Malama Shafa'atu Umar ta zargi yadda wasu bara-gurbi a yansiyasa, ke yaudarar mata ta hanyar sayen kuri'unsu da zimmar cewa, zasu mori romon dimokuraɗiyyar.

Kam da yawa a ke zargin wasu bata gari daga cikin Yansiyasa da shafawa mata maski a baki da makasudin haɓaka jam'iyyarsu ko kuma gurgunta abokan adawar su, wanda hakan kan janyo faduwar guzuma (Uwa kwance Ya kwance)

Comments

Popular posts from this blog

ATIKU YA GANA DA WAKILAN CIBIYAR KASA DA KASA TA REPUBLICAN DA CIBIYAR HARKOKIN DIMUKURADIYYA TA KASA, AN BADA SHAWARAR SAMAR DA TAKARDUN ZABE DA ZASU KAWAR DA SIYAN KURI'U

ATIKU YA SHA ALWASHIN TABBATAR DA DAIDAITUWAR TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA YAYIN YAKIN NEMAN ZABEN SA GOMBE