ATIKU YA SHA ALWASHIN TABBATAR DA DAIDAITUWAR TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA YAYIN YAKIN NEMAN ZABEN SA GOMBE
Dan Takarar shugabancin Najeriya na Jam'iyyar PDP a zaben badi Alhaji Atiku Abubakar yayin yakin neman zaben sa a Gombe ya yi alkawarin daidaita tattalin arzikin Najeriya idan aka zabe shi badi.
Da yake jawabi ga dandanzon magoya bayan sa da shugabannin Jam'iyya da jagorori a filin wasa na Gombe, tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alkawarin aiki domin inganta tattalin arzikin Najeriya da ci gaban ta.
Ya bawa mutanen Gambe tabbacin cewar gwamnatin sa zata farfado da Dam din Dadin Kowa inda ya yi kira ga mutanen jihar su bashi dama ya zama Tafawa Balewa na biyu, inda yace an shafe Lokaci Mai tsawo yankin Bai Samar da shugaban Najeriya ba.
Atiku ya ce zuwa Gombe kamar zuwa gida ne a wurin sa, ya kuma bada tabbacin warware matsalar tsaro a yankin tare da maido da zaman lafiya sannan ya farfado da tattalin arziki a dukkan matakai.
Masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar PDP a jihar ta Gombe sun bada tabbacin goyon baya ga Atiku da Jam'iyyar sa.
Da suke magana ta bakin shugaban Jam'iyyar na Gombe major A K Kwaskebe Mai ritaya sun Yi alkawarin aiki domin nasarar Jam'iyyar da Takarar ta Atiku Abubakar.
Sauran manyan Baki a taron sun bada tabbacin cewar sun yanke shawarar aiki tare domin aiwatar da alkawari da manufofin jam’iyar ta PDP. Sauran manyan bakin sun hada da gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom da Aminu Tambuwal na jihar Sokoto Wanda shi ne babban daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa. Sauran sun hada da Dr Ibrahim Dankwambo tsohon gwamnan jihar da gwamnan jihar Adamawa Ahamadu Ummaru Fintiri.
Sauran abubuwan da suka faru a wurin taron sun hada da mika tutar Takarar gwamna ga Muhammad Jibril Dan Barde Wanda ya nuna murnar sa bisa yadda aka tarbi Dan Takarar shugaban kasar.
Sannan ya bada tabbacin cewar gwamnatin Atiku zata Samar da tsaro da inganta tattalin arziki da Samar da ayyukan yi, farfado da harkokin Noma tare da hada kan kasa.
Wadan nan bayanai su na rattabe ne a cikin sanarwar da Abdulrasheed Shehu
(Mataimaki na Musamman ga Mai girma Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai) ya fitar a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamban 2023.
Comments
Post a Comment