ATIKU YA GANA DA WAKILAN CIBIYAR KASA DA KASA TA REPUBLICAN DA CIBIYAR HARKOKIN DIMUKURADIYYA TA KASA, AN BADA SHAWARAR SAMAR DA TAKARDUN ZABE DA ZASU KAWAR DA SIYAN KURI'U
Dan Takarar shugabancin Najeriya a Jam'iyyar PDP a zabe Mai zuwa Alh. Atiku Abubakar (GCON) ya yi wata ganawa yau a Abuja da wani ayarin hadin gwiwa daga cibiyar kasa da kasa ta republican da cibiyar harkokin demukuradiyya ta kasa NDI karkashin jagorancin Mr. Frank LaRose sakataren jihar Ohio ta Amurka. Wannan dai yana kumshe ne a cikin takardar bayan taro, wadda Mataimaki na Musamman ga Alh. Atiku Abubakar din kan Kafofin Watsa Labarai AbdulRasheed Shehu ya fitar. A taron, Wazirin Adamawa yace ya yi ganawa Mai muhimmancin gaske da ayarin, dangane da muhimmancin alfanun bunkasa dimukuradiyyar gaskiya a tsarin gudanar da zabe Musamman kare tsarin doka da oda da sauran batutuwa. Tsohon mataimakin shugaban kasar ta Najeriya yace a yayin tattaunawar tasu, ya bada shawarar Samar da takardun zabe na Musamman domin kawar da matsalar sayen kuri'u Wanda ke Neman zama ruwan dare a tsarin zabukan mu. A karshe taron, Dan Takarar ta PDP ya godewa bakin
Comments
Post a Comment