KUNGIYAR LIFE HELPERS TA WAYAR DA KAI AKAN ILLAR SAYEN KURI’A

Kungiyar life helpers din dai, ta gudanarda taron na wayar da kai da karawa juna sani ne, tare da shuwagabannin kungiyoyin mata na 100 women group leaders wadanda su ka fito daga kananan hukumomi 23 dake fadin Jahar sakkwato. Taron wanda aka shirya domin jan hankalin mata akan illar da ke tattare da sayar da kuri’a a lokutan zabe ya kuma tattauna batutuwa da suka shafi shigowar mata a dama da su a sha’anin siyasa da shugabanci. Malama Hadiza Yaro ita ce ta jagoranci zaman ta bayyana cewa wanan zaman na da alaka da taron da kungiyar ta yi a babban birnin tarayya Abuja tare da masu daukar nauyin wannan wayar da kan waton EU-ACT, taron da aka shirya domin fadakar da mata akan illolin da ke tattare da sayar da kuri’un su a lokutan zabe. Hadiza yaro ta bayyana cewa sun bayar da horo ga mata na kungiyar ta 100 women group akan illolin sayarda kuri’a inda ta ce suna kara jan kunne ga mata akan yin yarjejeniya da yan siyasa na ayukkan da za su yi a kamin a zabe su. Hadiza yaro ta kuma ja hankalinsu akan ka da su bari yan siyasa suyi amfani da su musamman a lokutan zabe ta hanyar ba su wasu yan kudade. Ta kuma ce yan siyasa za su ci gaba da farautar kungiyoyin mata musamman idan lokacin zabe ya tashi inda tace suyi amfani da wannan lokaci domin yin tsayin daka akan samar musu da ayukkan ci gaba maimakon rufe su karbi abin duniya. Fatima Larai Tahir, na daya daga cikin shuwagabannin kungiyoyin mata a jihar Sakkwato, ta bayyana irin kalubalen da mata suke fuskanta a lokacin siyasa musamman ta hanyar yin fatali da su bayan sun bada tasu gudunmuwa. Fatima ta ce sau tari da dama sun yi wahalhalu daban-daban amma kuma bayan samun mulki ba wanda zai waiwaye su. Ita ma da ta ke tofa albarkacin bakinta a yayin taron, Hajiya Yannare Yabo, ta nuna bukatar da ke akwai akan mata su maida hankali wajen kulla alkawurra da yan takara wajen aiwatar musu da ayukkan ci gaba maimakon ba su abin da bai taka kara ya karya ba.
Tace abu ne mai kyau mata su dukufa wajen yin yarjejeniya da duka yan takara na yankunansu akan yi musu ayukka ko kuma ma wadanni ayukka suka taba aiwatarwa. Hajiya Yannare ta ce kamata ya yi ‘yansiyasa masu neman kujeru su kasance masu son yin ayukka ga yankunan su maimakon nuna handama da babakere.

Comments

Popular posts from this blog

ATIKU YA GANA DA WAKILAN CIBIYAR KASA DA KASA TA REPUBLICAN DA CIBIYAR HARKOKIN DIMUKURADIYYA TA KASA, AN BADA SHAWARAR SAMAR DA TAKARDUN ZABE DA ZASU KAWAR DA SIYAN KURI'U

ATIKU YA SHA ALWASHIN TABBATAR DA DAIDAITUWAR TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA YAYIN YAKIN NEMAN ZABEN SA GOMBE