ATIKU YA KARBI YAYAN JAM'IYYAR APC DA SUKA SAUYA SHEKA DAGA JIHAR ZAMFARA

Dan Takarar shugabancin Najeriya a zaben badi karkashin Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya karbi wata tawagar yayan Jam'iyyar PDP daga jihar Zamfara karkashin jagorancin Dr. Dauda Lawan Wanda shi ne Dan Takarar gwamnan jihar na PDP.

Wannan yana kumshe ne a cikin wata takardar manema labarai da 
Abdulrasheed Shehu, 
Mataimaki na Musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai din ya fitar a ranar Laraba.
Kazalika cikin tawagar da ta ziyarci Wazirin na Adamawa sun hada da yan siyasar nan na APC da suka sauya sheka zuwa PDP Alhaji Salihu Mai Buhu Gummi da Alhaji I. Alhaji Bakuraa Sahabi Liman Kaura.

A jawabin sa, jagoran ayarin yace sun gamsu da akidun siyasar tsohon mataimakin shugaban kasar saboda kishin sa da kwazo da kuma manufarsa ta kaunar hada kan kasa da zaman lafiya da ci gaba, inda suka tabbatar wa da Dan Takarar ta PDP goyon bayan su a yunkurin sa na Gina ingantacciiyar kasa.
A nasa bangare, Dan Takarar shugabancin kasar na PDP Atiku Abubakar, yayin da yake gode musu bisa ziyarar, ya sake jaddada aniyar sa ta aiki tare da yayan Jam'iyyar da masu ruwa da tsaki a Zamfara da Najeriya gaba daya domin samun nasarar Jam'iyyar PDP a zaben 2023.

Comments

Popular posts from this blog

ATIKU YA GANA DA WAKILAN CIBIYAR KASA DA KASA TA REPUBLICAN DA CIBIYAR HARKOKIN DIMUKURADIYYA TA KASA, AN BADA SHAWARAR SAMAR DA TAKARDUN ZABE DA ZASU KAWAR DA SIYAN KURI'U

ATIKU YA SHA ALWASHIN TABBATAR DA DAIDAITUWAR TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA YAYIN YAKIN NEMAN ZABEN SA GOMBE