Posts

KUNGIYAR LIFE HELPERS TA WAYAR DA KAI AKAN ILLAR SAYEN KURI’A

Image
Kungiyar life helpers din dai, ta gudanarda taron na wayar da kai da karawa juna sani ne, tare da shuwagabannin kungiyoyin mata na 100 women group leaders wadanda su ka fito daga kananan hukumomi 23 dake fadin Jahar sakkwato. Taron wanda aka shirya domin jan hankalin mata akan illar da ke tattare da sayar da kuri’a a lokutan zabe ya kuma tattauna batutuwa da suka shafi shigowar mata a dama da su a sha’anin siyasa da shugabanci. Malama Hadiza Yaro ita ce ta jagoranci zaman ta bayyana cewa wanan zaman na da alaka da taron da kungiyar ta yi a babban birnin tarayya Abuja tare da masu daukar nauyin wannan wayar da kan waton EU-ACT, taron da aka shirya domin fadakar da mata akan illolin da ke tattare da sayar da kuri’un su a lokutan zabe. Hadiza yaro ta bayyana cewa sun bayar da horo ga mata na kungiyar ta 100 women group akan illolin sayarda kuri’a inda ta ce suna kara jan kunne ga mata akan yin yarjejeniya da yan siyasa na ayukkan da za su yi a kamin a zabe su. Hadiza yaro ta kuma ja han

ATIKU YA KARBI YAYAN JAM'IYYAR APC DA SUKA SAUYA SHEKA DAGA JIHAR ZAMFARA

Image
Dan Takarar shugabancin Najeriya a zaben badi karkashin Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya karbi wata tawagar yayan Jam'iyyar PDP daga jihar Zamfara karkashin jagorancin Dr. Dauda Lawan Wanda shi ne Dan Takarar gwamnan jihar na PDP. Wannan yana kumshe ne a cikin wata takardar manema labarai da  Abdulrasheed Shehu,  Mataimaki na Musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai din ya fitar a ranar Laraba. Kazalika cikin tawagar da ta ziyarci Wazirin na Adamawa sun hada da yan siyasar nan na APC da suka sauya sheka zuwa PDP Alhaji Salihu Mai Buhu Gummi da Alhaji I. Alhaji Bakuraa Sahabi Liman Kaura. A jawabin sa, jagoran ayarin yace sun gamsu da akidun siyasar tsohon mataimakin shugaban kasar saboda kishin sa da kwazo da kuma manufarsa ta kaunar hada kan kasa da zaman lafiya da ci gaba, inda suka tabbatar wa da Dan Takarar ta PDP goyon bayan su a yunkurin sa na Gina ingantacciiyar kasa. A nasa bangare, Dan Takarar shugabancin kasar na PDP Atik

ATIKU YA GANA DA WAKILAN CIBIYAR KASA DA KASA TA REPUBLICAN DA CIBIYAR HARKOKIN DIMUKURADIYYA TA KASA, AN BADA SHAWARAR SAMAR DA TAKARDUN ZABE DA ZASU KAWAR DA SIYAN KURI'U

Image
Dan Takarar shugabancin Najeriya a Jam'iyyar PDP a zabe Mai zuwa Alh. Atiku Abubakar (GCON) ya yi wata ganawa yau a Abuja da wani ayarin hadin gwiwa daga cibiyar kasa da kasa ta republican da cibiyar harkokin demukuradiyya ta kasa NDI karkashin jagorancin Mr. Frank LaRose sakataren jihar Ohio ta Amurka. Wannan dai yana kumshe ne a cikin takardar bayan taro, wadda Mataimaki na Musamman ga Alh. Atiku Abubakar din kan Kafofin Watsa Labarai AbdulRasheed Shehu ya fitar.  A taron, Wazirin Adamawa yace ya yi ganawa Mai muhimmancin gaske da ayarin, dangane da muhimmancin alfanun bunkasa dimukuradiyyar gaskiya a tsarin gudanar da zabe Musamman kare tsarin doka da oda da sauran batutuwa. Tsohon mataimakin shugaban kasar ta Najeriya yace a yayin tattaunawar tasu, ya bada shawarar Samar da takardun zabe na Musamman domin kawar da matsalar sayen kuri'u Wanda ke Neman zama ruwan dare a tsarin zabukan mu. A karshe taron, Dan Takarar ta PDP ya godewa bakin

Jikan Babi Production Studio

Image
The new Jikan Babi Production recording studio is set for grand opening.